
Za mu ƙona motoci 250 muddin ba a bamu makamanmu ba – Ƴan ta’adda
Wasu Ƴan ta'adda a Jihar Zamfara da ke Najeriya sun yi barazanar ƙona motoci 250 sakamakon harin da aka kai musu a Ƴankin Ɗansadau, inda aka kashe wasu daga cikinsu tare da ƙwace bindigoginsu da kuma babura.
Sanarwar da ƴan ta'addan suka yi, na zuwa ne bayan fara ƙona motocin da suka yi, inda suka ce dole sai an dawo musu da bindigogi da kuma babur ɗin da aka kwace, yayin da suka fara kai hari wasu ƙauyuka.
Kan wannan lamari Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da ɗaya daga cikin Dattawan Najeriya da suka fito daga yankin, Sanata Sa’idu Ɗansadau.
Sai a latsa alamar sauti da ke sama domin sauraron…
The skinny
The skinny isn't ready yet — notes appear once the transcript is processed.