skinny.

Latest / Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Emoud Issif kan janye shirin ƙara kuɗin man fetur a Nijar

Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun jingine batun ƙara farashin mai, bayan da a can da farko ministan makamashi ya ce gwamnati na kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayo mai daga ƙetare don cike giɓin da ƙasar ke fuskanta.

Duk da cewa ana haƙowa da kuma tace shi ne a cikin gida, amma an share makonni da dama ana fama da ƙarancin mai a Nijar.

Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Emoud Issif, mamba a Majalisar Tuntuɓa ta ƙasar, wadda ita ce ta bayar da shawarar a yi wannan ƙarin amma gwamnati ta yi watsi da ita, inda ya ce tun da farko ba sa daga cikin masu goyon bayan shawarar.

Ku latsa alamar sauti don…

Log in to save or queue this episode.

The skinny

The skinny isn't ready yet — notes appear once the transcript is processed.